Ubanmu Ya Tona Annabin Ƙarya
Hananiya ya sanar a gaban jama'a cewa karkiyar Babila za ta karye cikin shekara biyu, ya kuma karya sandar karkiyar Irmiya don ya tabbatar. Irmiya ya amsa da Amin, sa'an nan ya dawo da karkiyar ƙarfe ta Ubanmu a maimakon ta itace, ya ce wa Hananiya zai mutu saboda koya wa jama'a su dogara ga ƙarya. Haka kuwa ya mutu.
28 1A shekarar nan, da farkon mulkin Zedekiya sarkin Yahuda, a shekara ta huɗu, a wata na biyar, sai Hananiya annabi ɗan Azzur daga Gibeyon ya gaya mini a cikin gidan Ubanmu, a gaban firistoci da dukan mutane, ya ce, 2“Ga abin da Ubangiji mai runduna na Sama, Allah na Isra'ila, yake cewa, ‘Na kakkarya karkiyar sarkin Babila. 3A cikin shekara biyu zan komo da dukan kayayyakin gidan Ubangiji zuwa wannan wuri, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babila ya ɗauka daga nan zuwa Babila. 4Haka kuma zan komo da Yekoniya ɗan Yehoyakim, sarkin Yahuda, da dukan bayin Yahuda da aka kai Babila zuwa nan, in ji Ubangiji, gama zan kakkarya karkiyar sarkin Babila.’”
5Sai Irmiya annabi ya amsa wa Hananiya annabi a gaban firistoci da dukan mutanen da suke tsaye a cikin gidan Ubanmu. 6Irmiya annabi ya ce, “Amin! Ubanmu yă yi haka. Yă tabbatar da kalmomin da ka yi annabci, ta wurin komo da kayayyakin gidan Ubanmu da dukan bayi daga Babila zuwa wannan wuri. 7Amma ka saurari wannan magana da nake yi maka, da kuma ga dukan waɗannan mutane yanzu, 8Annabawan da suka riga mu tun dā sun yi annabci game da yaƙi, da masifa, da annoba a kan al'ummai masu yawa, da manyan mulkoki. 9Annabin da ya yi annabci game da salama kuwa, sai sa'ad da maganarsa ta cika ne za a tabbatar da shi hakika Ubanmu ne ya aike shi.”
10Sai Hananiya annabi ya ɗauki karkiyar daga wuyan Irmiya annabi ya kakkarya ta, 11Hananiya kuma ya gaya wa dukan mutane, ya ce, “Ga abin da Ubangiji yake cewa, ‘Haka zan kakkarya karkiyar Nebukadnezzar sarkin Babila daga wuyan dukan al'ummai a cikin shekara biyu.’” Sa'an nan Irmiya annabi ya tafi abinsa.
12Bayan Hananiya ya kakkarya karkiyar daga wuyan Irmiya annabi, sai maganar Ubanmu ta zo wa Irmiya, ta ce,
13“Je ka, ka gaya wa Hananiya cewa, Ubanmu ya ce, ‘Ka kakkarya karkiyar itace, amma za ka yi ta ƙarfe a maimakonsu. 14Gama ga abin da Uba mai runduna na Sama, Ubanmu na Isra'ila, yake cewa, Na sa karkiyar ƙarfe a kan wuyan dukan waɗannan al'ummai domin su bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babila, su kuwa za su bauta masa. Har ma na ba shi dabbobin jeji.’”
15Sai Irmiya annabi ya ce wa Hananiya annabi, “Ka saurara, Hananiya! Ubanmu bai aike ka ba; ka sa wannan jama'a su dogara ga ƙarya.
16Saboda haka ga abin da Ubanmu yake cewa, ‘Zan kawar da kai daga duniya a wannan shekara; za ka mutu domin ka yi wa'azin tawaye ga Ubanmu.’”
17Hananiya annabi kuwa ya mutu a wannan shekara, a wata na bakwai.