Bayarwa don Iyalin da suke cikin Bukata
Rufewa ta aiki: ku keɓe kuɗi kowane mako domin tarawar Urushalima don kada a yi gaggawa sa'ad da Bulus ya iso. Yana shirin zama na dogon lokaci bayan Makidoniya, ya yaba wa Timoti da gidan Istifanas, ya kuma taƙaita wasiƙar — ku ƙarfafa, bari kuma a yi kome cikin ƙauna.
16 1Game da tarin kuɗi saboda tsarkaka, ku yi kamar yadda na umarci ikkilisiyun Galatiya. 2A rana ta fari ta kowane mako, kowannenku yă keɓe wani abu, yana ajiyewa gwargwadon yadda ya yi arziki, don kada a yi tarin kuɗi sa'ad da na zo. 3Sa'ad da na zo, zan aiki waɗanda kuka amince da su, tare da wasiƙu, su kai kyautarku Urushalima. 4In kuwa ya dace in tafi ni ma, to, za su tafi tare da ni.
Shirye-shiryen Bulus na Ziyara
5Zan zo wurinku bayan na ratsa Makidoniya, gama zan bi ta Makidoniya, 6amma wataƙila in zauna tare da ku, har in ci lokacin sanyi, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda zan tafi. 7Ba na so in yi ziyarar wucewa kawai yanzu; ina begen in zauna tare da ku na ɗan lokaci, in Ubangiji ya yarda. 8Amma zan zauna a Afisa har Fentikos, 9gama an buɗe mini wata faffadar ƙofa don aiki mai amfani, akwai kuma maƙiya da yawa.
10Sa'ad da Timoti ya zo, ku tabbata ba ya jin tsoro a cikinku, gama yana aikin Ubangiji ne, kamar yadda ni nake yi. 11Saboda haka kada kowa yă rena shi. Ku sallame shi lafiya yă zo wurina, gama ina sa ran zuwansa tare da 'yan'uwa.
12Game da ɗan'uwanmu Afollos, na matsa masa sosai yă zo wurinku tare da 'yan'uwa, amma bai yarda ko kaɗan yă zo yanzu ba; zai zo sa'ad da ya sami dama.
13Ku zauna a faɗake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, ku yi ƙarfin hali, ku yi ƙarfi. 14Duk abin da kuke yi, sai a yi shi cikin ƙauna.
15Yanzu ina roƙonku, 'yan'uwa, kun san iyalin Istifanas su ne nunan fari na Akaya, sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima, 16ku yi biyayya ga irin waɗannan mutane, da kuma ga duk mai haɗa kai a aiki da famar yi. 17Ina farin ciki da Istifanas, da Fortunatus, da Akaikus sun zo, domin sun cika gurbin rashinku, 18gama sun wartsake ruhuna da naku. Ku ba irin waɗannan mutane girma.
Gaisuwa daga Iyali
19Ikkilisiyun Asiya suna gaishe ku. Akila da Firiskila, tare da ikkilisiyar da take gidansu, suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji. 20Dukan 'yan'uwa suna gaishe ku. Ku gai da juna da sumba mai tsarki.
21Ni Bulus, na rubuta wannan gaisuwa da hannuna. 22Idan wani ba ya ƙaunar Ubangiji, to, yă zama la'ananne. Ubangijinmu, ka zo! a a v22 Maranata ita ce addu'a ta farko ta ikkilisiya a harshen Aramiyanci — “Ubangijinmu, ka zo!” — kukan marmari ga Yesu yă dawo. 23Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku. 24Ƙaunata tă kasance tare da ku duka cikin Almasihu Yesu. Amin.